Messi bai ji rauni ba, in ji likitocin Barca

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barca za ta kara karawa da Athletico Bilbao a gasar Copa del Rey a ranar Laraba

Likitocin Barcelona sun bayar da tabbacin cewar Lionel Messi bai ji rauni ba a karawar da suka doke Athletic Bilbao da ci 6-0 a gasar La Liga ranar Lahadi.

Messi, mai shekara 28, shi ne ya fara cin kwallo a wasan, amma aka sauya shi domin kada ya samu matsala a karawar.

A wani bincike da likitocin Barca suka gudanar da safiyar Litinin ya nuna cewar dan kwallon ya dan bugu ne a fafatawar, kuma zai iya ci gaba da buga wasanni.

Barcelona ta ce ba ta da tabbacin idan za ta saka Messi a wasan da za su buga da Athletic Bilbao a gasar Copa del Rey ranar Laraba.