Inter Milan ta soke yarjejeniya da Vidic

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nemanja Vidic tsohon dan wasan Manchester United

Inter Milan ta soke yarjejeniyar da ke tsakaninta da Nemanja Vidic, bayan da ya kasa buga wasa a kakar bana.

Dan wasan, mai tsaron baya mai shekara 34 ya koma Inter ne daga Manchester United a 2014.

Dan kwallon tawagar Serbia ya buga wa Inter wasanni 28 a kakar wasan bara.

Vidic ya lashe kofunan Premier biyar da kofin zakatun Turai a shekara takwas da rabi da ya murza leda a Old Trafford.