Austalia Open: Djokovic ya kai wasan gaba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Novak ne ke rike da kofin Australian Open na bara

Mai rike da kofin kwallon tennis na Australian Open, Novak Djokovic, ya kai wasan zagaye na biyu, bayan da ya doke Quentin Halys da ci 6-1, 6-2, 7-6.

Ita ma Serena Williams ta kai wasan zagaye na uku, bayan da ta samu nasara a kan Su-Wei Hsieh da ci 6-1, 6-2.

Shi ma Roger Federer da Maria Sharapova sun kai wasan zagaye na uku a gasar ta Australia Open.

Sai dai kuma wadda ta lashe gasar Wimledon karo biyu, Petra Kvitova, ta sha kashi a hannun Daria Gavrilova da ci 6-4, 6-4

A ranar Alhamis ne Andy Murray da Johanna Konta za su buga wasan zagaye na biyu a gasar.