CHAN 2016: Rwanda ta kai wasan daf da na karshe

Hakkin mallakar hoto Dareen Mckinstry
Image caption Rwanda ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar cin kofin Afirka

Mai masaukin baki Rwanda ta kai wasan daf da na karshe a gasar cin kofin Afirka ta 'yan wasan da ke murza-leda a nahiyar.

Rwanda ta kai wasan zagaye na gaba a gasar ne, inda ta ci Gabon 2-1 a karawar da suka yi a Kigali wasan na biyu na rukunin farko ranar Laraba.

Ernest Sugira ne ya ci wa Rwanda kwallon farko kafin a tafi hutun rabin lokaci, bayan kuma da aka dawo ya kara cin ta biyu.

Gabon ta farke kwallo daya ne ta hannun Aaron Boupendza a minti na takwas da dawo wa daga hutun rabin lokaci.

A ranar Lahadi ne Rwanda za ta fafata da Morocco da kuma karawar da za a yi tsakanin Ivory Coast da Gabon a wasa na karshe na rukunin farko.