Athletico Bilbao za ta gwabza da Barcelona

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a ci gaba da wasan daf da na karshe a Copa del Rey a Spaniya

Athletico Bilbao za ta karbi bakuncin Barcelona a gasar Copa del Rey wasan daf da na kusa da karshe a ranar Laraba.

Barcelona -- wadda ke rike da kofin bara -- ta kai wannan matakin ne bayan da ta doke Espanyol da ci 2-0.

Ita kuwa Athletico Bilbao ta kai wannan matsayin ne bayan da ta ci Villareal da ci daya mai ban haushi.

Barcelona ce ta doke Athletico Bilbao da ci 3-1, ta kuma lashe kofin bara, watau sau 27 ke nan.

Haka kuma Celta de Vigo da Atletico Madrid za su kece raini a wasan daf da na karshe a gasar.