Super 4: Enyimba da Nasarawa sun buga 1-1

Hakkin mallakar hoto npfl twitter
Image caption Jihar Kaduna ce ke karba bakuncin wasannin farko na Super 4

Enyimba International ta tashi 1-1 da Nasarawa United a gasar wasan Super 4 da suka kara a Kaduna ranar Laraba.

Enyimba ce ta fara cin kwallon ta hannun Osadiaye daga bugun tazara saura minti 10 a tafi hutun rabin lokaci.

Nasarawa United ta farke kwallon ta hannun Azango daf da za a tashi daga karawar.

Wasa na biyu kuwa Warri Wolves ce ta doke Akwa United da ci daya mai ban haushi.

Za kuma a buga wasannin gaba tsakanin Akwa United da Enyimba, da kuma wasa tsakanin Nasarawa United da Warri Wolves ranar Juma'a 22 ga watan Janairu.