Wasan Llyton na karshe bai kyau ba

Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Lyton Hewitt

Llyton Hewitt ya sha kasa a wasansa na karshe na shi kadai bayan da David Ferrer ya lallasa shi, a zagaye na biyu na gasar wasan Tennis ta Australia Open.

Llyton Hewit wanda ya dauki kofuna har biyu na irin gasar dai ya kwashi kashinsa a hannun Ferrer ne da ci 6 da 2 da 6 da 4 da kuma 6 da 4.

A baya dai Hewitt ya samu nasarar cin wasannin nasa na shi kadai har sau 30 kuma ya yi nasara a gasar wasannin kwallon tennis din ta US Open, a 2001 da Wimbledon a 2002.

Ya kuma taka rawar gani wajen ganin kasarsa ta Australia ta dauki kambun wasan gasar tennis ta Davis Cup har karo biyu, a 1999 da 2003.