Buhari ya karrama 'yan wasan Nigeria

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Buhari ya cika alkawari bayan shekaru 30

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wani buki na karrama 'yan wasan kasar wadanda suka samu nasarori a wasanni tare da jami'ansu.

A lokacin bukin shugaba Buhari ya yi godiya ga Allah da ya bashi damar kawowa wannan lokacin da zai cika alkawarin da ya yi wa 'yan wasan kwallon kafa na kasar wadanda suka ci kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 17 a shekarar 1985.

An dai ba da rahoton cewa an bai wa 'yan wasan wadanda suka ci wannan kofi a shekarar 1985 naira miliyan bi-biyu, yayin da su kuma wadanda suka samu nasarar cin kofin na 'yan kasa da shekaru 17 a bara, aka ba su naira miliyan dai-dai da rabi.

Haka nan kuma an bai wa wasu 'yan wasan daban-daban tare da jami'ansu kyaututtuka na kudi kamar yadda yake kunshe a jaddawalin kyauta na ma'aikatar wasanni.