Mascherano yana gudun shiga kurkuku

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Javier Mascherano

Mai tsaron bayan kulob din Bercelona, Javier Masherano ya bayyana a gaban kotu domin neman taa hana a sanya shi a kurkuku, kan badakalar kudin harajin da ya kai Yuro miliyan daya da dubu dari.

Dan wasan mai shekara 31, ya amince da laifuka biyu da ake tuhumar sa da su masu alaka da almundahanar kin bayyana ilahirin kadararsa 2011 da 2012.

Yanzu haka dai kotu za ta yanke ko dai Mercherano zai iya biyan karin kudin tara a kan wadda ya biya a baya domin guje wa zuwa gidan maza, ko kuma a'a, kamar yadda rahotanni daga kasar Spain suka ce.

A na dai zargin sa da kokarin boye abin da yake samu daga kamfanonin da yake da su a kasashen waje.

Wata kotu dai ta tabbatar da cewa Mascherano ya biya kudi Yuro miliyan daya da dubu dari bakwai.