Karo na 11 a jere, Real Madrid ce ma fi arziki a duniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kulob din Real Madrid ya mallaki Fam miliyan 577.

A karo na goma sha daya a jere, an ayyana Real Madrid a matsayin kulob din da ya fi kowanne kulob kudi a duniya.

Kamfanin Deloitte da ke tantance yawan dukiyar da manyan kulob 20 suka mallaka ya ce a kakar shekarar 2014-2015, ya kiyasta cewa kudaden shiga na dukkan kulob-kulob din guda 20 sun bunkasa zuwa kashi takwas cikin dari, watau sun samu Dala biliyan biyar da miliyan dari daya.

A cewar Deloitte, kulob din Barcelona shi ne ya zo na biyu a jerin kulob-kulob din da suka fi kudi, yayin da Manchester United ke a matsayi na uku. Kazalika, Paris Saint-Germain da Bayern Munich su ne na hudu da na biyar. Manchester City da Arsenal da Chelsea da Liverpool su ne ke matsayi na shida da na bakwai da na takwas da kuma na tara, inda suka samu karuwar kudaden shiga.

Tottenham ne na 12, yayin da Newcastle da Everton ke matsayi na 17 da na 18.

Haka kuma a karon farko tun daga kakar wasanni ta shekarar 2005-2006, kulob din West Ham ya shiga jerin kulob-kulob din da suka fi kudi a duniya, inda y azo na ashirin.

Kamfanin ya yi nazari ne kawai kan kudaden shigar da kulob-kulob suka samu, ban da bashin da ake bin su ba.

  1. Real Madrid : £577m
  2. Barcelona: £560.8m
  3. Man Utd : £519.5m
  4. Paris Saint Germain : £480.8m
  5. Bayern Munich: £474m
  6. Mancheter City: £463.5m
  7. Arsenal: £435.5
  8. Chelsea; £420m
  9. Liverpool: £391.8m
  10. Juventus: £323.9m