Shin United na son Guardiola ya zama kociyanta?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kulob din United ya ce ba ya zawarcin Guardiola.

Kulob din Manchester United ya musanta cewa wakilansa sun gana da kociyan Bayern Munich, Pep Guardiola, domin ganin ya koma United a matsayin mai horas da 'yan wasa.

Shafin intanet na France Football ya ruwaito cewa wakilan United da Guardiola sun gana ne a makon jiya a birnin Paris, sai dai United ya karyata labarin.

Guardiola, mai shekara 45, zai bar Bayern Munich a lokacin hunturu, kuma ya ce kulob din Turai da dama suna son su dauke shi aiki.

Manchester City ne kan gaba cikin kulob din da ake sa ran za su dauke shi aiki, sai kuma Chelsea da United da ake rade-radin na son daukarsa.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da makomar Van Gaal a Old Trafford ke fuskantar rashin tabbas.