Zarate ya koma Fiorentina daga West Ham

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zarate ya ci United a wasansu da West Ham

Dan kwallon Argentina, Mauro Zarate ya fice daga West Ham inda ya koma kungiyar Fiorentina ta Italiya.

Dan shekarun 28, ya koma West Ham ne daga Velez Sarsfield a shekarar 2014 kafin a bayar da aronsa zuwa kungiyar QPR.

A kakar wasa ta bana Zarate ya zura kwallaye biyar a wasanni 21 da ya buga wa West Ham.

"West Ham na godiya ga Mauro saboda kokarinsa kuma muna yi masa fatan alheri," in ji Sanawar Hammers.