Liverpool ta doke Norwich

Hakkin mallakar hoto reauters
Image caption Liverpool na murna

Dan wasan kungiyar Liverpool, Adam Lallana ne ya ci kwallo ta biyar a mintin karshe, abin da ya dora Liverpool akan Norwhich.

Kafin Lallana ya jefa kwallon ta biyar dai kungiyoyin biyu sun yi chanjaras da ci 4 da 4.

Roberto Firmino shi ya fara daga ragar Norwich, kafin Dieumerci Mbokani na Norwich ya rama wa kungiyar tasa sannan kuma Steven Naismith ya kara ta biyu.

Wes Hoolahan ne ya kara jefa kwallo ta uku a ragar ta Liverpool, amma daga baya Jordan Henderson da Firminho kowannensu ya samu dabar jefa kwallo guda a ragar Norwich.

James Milner ne ya ci wa Liverpool kwallo ta hudu, kafin dan wasan Norwich Sebastian Bassong shi ma ya rama wa kulob din nasa.