Australian Open: Djokovic ya tsallake rijiya da baya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Novak Djokovic

Mai rike da kambun gasar Tennis ta duniya, Novak Djokovic ya tsallake rijiya da baya a inda ya lallasa Gilles Simon, a minti 16 na karshe.

Wannan ya ba shi damar zama mutum na takwas da suka raga a gasar Tennis ta Australian Open da ke gudana a Melbourne.

Djokovic din dai ya lallasa Gilles Simon ne da ci 6 da 3 da 6 da 7 da kuma 6 da 4 da 4 da 6 da 6 da 3.

Djokovic, mai shekara 28 wanda ya zama zakara na irin gasar har karo biyar a baya, yana kokarin kai wa wasan dab-da-na-kusa-da-na-karshe karo na 27 a jere.