Man Utd ba ta yi katabis ba - David

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption David Gill

Tshohon shugaban kungiyar wasa ta Manchester United, David Gill, ya ce kulob din bai katabis ba a wasannin Premier na wannan kakar, kuma yana fatan abubuwa za su gyaru.

A ranar Asabar dai Manchester United din ba ta ji da dadi ba a hannun Southampton bayan ci daya mai ban haushi da aka yi mu su a gida.

Wannan dai shi ne karo na shida da Man Utd din take rashin sa'a a wasanninta. Kuma yanzu haka akwai tazarar maki biyar tsakanin kungiyar da kulob mai mataki na hudu a kan teburin Premier, Tottenham.

Bayan da mai busa ya busa tashi a wasan da Southampton ta ci Man Utd din daya a gidanta, sai 'yan kallo suka fara yi wa 'yan wasan Man Utd ihu.