'Mourinho bai rubuta wa Man Utd wasika ba'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jose Mourinho har yanzu ba shi da kulob

Wani wakilin Jose Mourinho, Jorge Mendes ya bayyana batun a ce Mourinho ya rubuta wasika mai shafi shida zuwa ga kulob din Manchester United yana neman ya gaji Louis van Gaal, a matsayin manajan kungiyar, da soki-burotso.

Jaridar Independent ta ranar Lahadi ta yi ikrarin cewa Mourinho ya yi sharhi kan badakalar 'yan wasan kungiyar Old Trafford a cikin wata wasika da jaridar ta kira takardar neman gindin zama ga kulob din.

Mourinho mai shekara 52 dai ya kasance kara-zube tun bayan da kulob din Chelsea ya kore shi, a watan Disamba.

A ranar Asabar ne dai 'yan kallo suka yi wa 'yan wasan Man Utd a tile sakamakon ci daya mai ban haushi da Southampton suka yi mu su, a gida.