Australian Open: Serena da Sharapova za su fafata

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Serena da Sharapova

Mai rike da kambun wasan Tennis ta duniya ajin mata, Serena Williams za ta fafata da Maria Sharapova a wasan dab-da-na-kusa-da-karshe na gasar Tennis ta Australian Open da ake yi a Melbourne.

Dukkannin matan biyu dai sun samu nasara a wasanninsu 16 na karshe, a ranar Lahadi.

Willam dai wanda ta lallasa Sharapova a wasan karshe na bara, ta ba wa Margaritra Gasparyan kashi da ci 6 da 2 da 6 da 1 a minti 55.

Serena wadda 'yar Amurka ce tana hakon cin gasar karo na 22 sannan kuma na bakwai a Melbourne.