Swansea ta casa Everton a gida

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andrew Ayew

A karon farko Swansea ta samu nasara a kan Everton kuma a gidanta.

Dan wasan Swansea Gylfi Sigurdsson ne ya fara daga ragar Everton a dukan daga kai mai tsaron raga, kafin daga bisani Gareth Barry shi ma ya ciwo wa kulob din nasa.

Sai dai kuma Andre Ayew ya raba gardama bayan da ya jefa kwallo ta biyu a ragar Everton.

Wannan ne dai karon farko da Swansea ta samu dama a kan Everton, kuma a karon farko da kulob din ya samu nasarar cin wasanni a jere a gasar Premier ta wannan kakar. A ranar Litinin Swansea din ta ci Watford daya da nema.

Yanzu Swansea ta kasance a mataki na 17 a teburin gasar Premier.