Mun sake fadawa tarkon Diego Costa - Wenger

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kociyan Arsenal, Arsene Wenger

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya ce kungiyarsa ta kara fadawa tarkon dan wasan Chelsea, Diego Costa bayan da dan wasan Arsenal din Per Mertesacker ya sami jan kati, a wasan da kungiyoyin biyu suka yi ranar Lahadi.

An ba wa Mertesacker jan kati a minti na 18 da fara wasa bayan da ya tade Diego Costa wanda kuma shi ne ya zura wa Arsenal kwallon da aka ci a wasan.

Arsene Wenger ya ce " Costa ya yi sanadiyyar korar 'yan wasanmu guda biyu a wasanni biyu da mu ka yi da Chelsea."

Costa dai ya yi sanadiyyar samun jan kati da dan wasan Arsenal, Gabriel ya yi a lokacin wasanni biyu da Chelsea ta ci Arsenal a watan Satumba.