'Drogba ba zai koma Chelsea ba'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Drogba ya kalli wasan Chelsea tare da Hiddink

Mahukunta a kungiyar Montreal Impact sun ce Didier Drogba zai ci gaba da murza leda a kulob din, lamarin da ya kawo karshen rade-radin da ake yi cewa dan wasan na shirin komawa Chelsea.

Kungiyar Montreal ta ce dan wasan zai halarci wajen atisayen da 'yan wasan za su yi gabanin a fara kakar wasa ta bana.

Shi kansa Drogba, mai shekara 37, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa "Ina kan hanya ta zuwa Qatar domin shiryawa kafin mu fara yin atisaye."

A watan Disamba ne Drogba ya tattauna da masu Chelsea a daidai lokacin da ake yin rade-radin cewa zai sake komawa kulob din domin zama daya daga cikin masu horas da 'yan wasa.