Ramires zai bar Chelsea

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ramires Sontos

Dan wasan tsakiya na Chelsea Ramires Santos yana gab da koma wa kulob din kasar China, Jiangsu Suning kan kudi kusan fan miliyan 25.

Dan wasan mai shekara 28 ya zo Chelsea ne daga Benfica a kan kudi fan miliyan 17 a 2010.

Ramires dai ya rattaba hannu a kan wani sabon kwantaragin da Chelsea, a watan Octoban 2015, sai dai kuma ya buga wasanni bakwai ne kacal a kakar wasan Premier.

Shi dai kulob din na Jiangsu ya zo na tara a gasar manyan kungiyoyin wasan China a 2015 sannan kuma ya dauki kofin kasar na shekarar.

Tsohon kociyan Chelsea ne, Dan Petrescu ya ke shugabancin kulob din.