Russia ta haramta wa mutum hudu wasa

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Irina Maracheva

Kwamitin wasannin Olympics na Russia ya haramta wa 'yan wasan tseren kasar su hudu wasa saboda samun su da shan kwayoyi masu kara kuzari.

Tsohuwar wadda ta dauki azurfa a gasar tseren mita 800 ta turai, Irina Maracheva na daya daga cikin mutanen, a inda aka haramta mata wasanni har na tsawon shekara biyu.

Sauran sun hada da Anna Lukyanova, wadda ita ma ta fuskanci haramcin shekara biyu, yayin da kuma Maria Nikolaeva da Elena Nikulina suka samu haramcin shekara hudu kowaccensu.

Wannan dai shi ne hukuncin farko da kwamitin gasar wasannin Olympics na kasar ya zartar tun bayan hana Russia shiga gasar wasannin tsere a watan Nuwamba.