Tennis: 'Yan Birtaniya biyu sun kai gaci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Johanna Konta

A karin farko cikin shekara 39, 'yan kasar Birtaniya mace da namiji suka samu damar kaiwa ga wasan dab-da-na-kusa-da-na-karshe na gasar tennis ta Ausralian Open.

'yan wasan dai su ne Johanna Konta da Andy Murray.

Johanna Konta dai ta zamo mace ta farko 'yar Birtaniya da ta kai wasan dab-da-na-kusa-da-karshe na gasar ta duniya, a tsawon shekaru 32, bayan da ta lallasa Ekaterina Makarova a gasar Australian Open din.

Shi ma Andy Murray ya kai wasan dab-da-na-kusa-da-na-karshe bayan da ya yi nasara a kan dan wasan Australia, Bernard Tomic da ci 6 da 4 da wata 6 da 4 da kuma 7 da 6.