Ban kyauta ba - van Gaal

Image caption Kociyan Man Utd, Louis van Gaal

Kociyan Manchester United, Louis van Gaal ya ce bai yi abin da ya dace ba, bayan da 'yan kallo suka yi wa 'yan wasansa ihu sakamakon cinsu da kungiyar Southampton ta yi 1- 0 ranar Asabar.

van Gaal ya ce " sun ci buri a kaina, amma ban iya cika mu su burin nasu ba, saboda haka raina ya baci sosai."

Ya kara da cewa " magoya baya suna da damar da za su yi ihu, amma dai komai dadi komai wuya muna tare."

Yanzu dai Man Utd ita ce ta biyar a teburin Premier, sannan akwai tazarar maki biyar tsakaninta da Tottenham wadda ita ce mai matsayi na hudu a teburin.

Manchester United dai ta samu maki 37 a wasanninta 23 na farko, wanda kuma wannan shi ne mafi kankantar maki da ta taba samu a gasar Premier.