CHAN: Guinea ta fitar da Nigeria

Hakkin mallakar hoto CAF

Guinea ta lallasa Najeriya da ci daya mai ban haushi, a wasan rukuni na uku wato Group C, na gasar cin kofin Afirka ta 'yan wasan cikin gida wato CHAN.

A baya dai Najeriya ta kasance gaba a rukunin, a inda take da maki 4, ita kuma Guinea ta ke da maki 2.

Amma a wasan da aka yi da yammacin Talatar nan, reshe ya juye da mujiya a inda Guinea ta samu maki 5, a inda ita kuma Tunisia ta samu maki 5 bayan ta ci Niger 4-0.

Yanzu dai Najeriya da Niger sun dawo gida, a inda su kuma Tunisia da Guinea sun ka cancanci zuwa wasan gaba.