Ban ce zan yi murabus ba - Van Gaal

Image caption Van Gaal ya musanta batun barin Manchester United

Kociyan Manchester United, Loius Van Gaal, ya musanta rade-radin da ake yi cewa ya yi niyyar barin aikinsa a karshen makon nan, duk da rahotannin da suka tabbatar da hakan.

An dai ruwaito cewa Van Gaal, mai shekaru 64, ya shaida wa mataimakin mai kulob din, Ed Woodward, cewa yana shirin barin kulob din bayan da Southampton ta lallasa su da ci1-0 a ranar Asabar.

Wasu majiyoyi sun tabbatarwa da BBC cewa ba a yi wannan tattaunawa tsakaninsu ba.

A ranar Talata ne Van Gaal zai ci gaba da yin atisaye da 'yan wasan kulob din a lokacin da za su fara shirye-shiryen buga karo na hudu na wasan cin kofin FA ranar Juma'a.

Masu kulob din na son ci gaba da kulle bakunansu a kan makomar Louis Van Gaal.