Rashawa ta mamaye hukumar Tennis

Wasan Tennis
Image caption Badakalar cin hanci da rawasha ta maamye hukumar wasanni ta duniya.

Hukumar kwallon Tennis ta duniya ta sanar da cewa za a gudanar da wani bincike a kan tasirin matakan hukumar na hana cin hanci da rashawa a harkokin Tennis.

Hukumar ta yi wannan sanarwar ne a wajen gasar Autralia Open, kuma sanarwar ta biyo bayan binciken da BBC da Buzzfeed News suka yi, wanda ya gano cewa ana zargin mutune 16 daga cikin fitattun 'yan wasan Tennis na duniya 50 da hannu a badakala ko ha'incin sayar da wasa.

A cewar hukumar, wani masanin dokokin wasanni dan Birtaniya ne zai jagoranci kwamitin binciken.

Shugaban hukumar Tennis Intergrity Philip Brook, yace ya zama wajibi a gudanar da binciken dan daukar matakin gaggawa tun kafin abun ya zama babba.