Townsend zai koma Newcastle

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Townsend yana gaisawa da kocin Ingila

Kulob din Newcastle ya yarda ya karbi dan wasan Tottenham, Andros Townsend a kan kudi Fan miliyan 12.

Townsend, mai shekara 24 ya buga wasanni uku ne kacal a gasar Premier a wannan kakar.

Dan wasan dan kasar Ingila ya buga wa kasar tasa wasanni 10, amma an ajiye shi a watan Nuwamba, lokacin gasar Europa, bayan da ya bata da mai horas da su motsa jiki, Nathan Gardiner.

Da ma dai Newscastle na neman 'yan wasan tsakiya guda biyu, Jonjo Shelvey da Henri Saivet a kasuwar saye da sayarwar 'yan wasa ta watan Janairu.