Boxing: An gargadi Fury kan kalaman batanci

Image caption Fury Tyson

Hukumomin wasanni sun ja kunnen zakaran damben Boxing ajin masu nauyi, Tyson Fury da ya guji yin maganganun da ba su da alaka da wasan dambe.

Hukumar kula da wasan dembe ta Birtaniya ce ta yi gargadin a karshen wani zama da ta yi.

Shi dai Fury, dan shekara 27, ya nemi afuwa bayan kalaman batanci da ya yi a kan mata da maza masu neman jinsi guda.

Kusan mutane dubu 140 ne suka rattaba hannu a kan wani koke na neman da a cire sunan Fury daga jerin manyan 'yan wasan da BBC ta zaba, kafin karrama su a watan December.