Dalilin da ya sa ban kalli fanareti ba - Klopp

Image caption Jurgen Klopp, kociyan Liverpool

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya ce magoya bayan kungiyarsa ne suka hana shi ya kalli bugun na da-kai-sai-mai-tsaron-gida da kulob din nasa ya yi da Stoke City, a gasar Carling Cup.

Klopp ya ce " Magoya bayan Liverpool sun ce na yi tsawo da yawa saboda haka ina kare mu su, shi yasa ban ga ko da bugu daya ba, ina bayan 'yan wasana sun yi min shinge."

Liverpool din dai ta samu nasarar jefa kwallaye 6, a bugun fanaretin, a inda ita kuma Stoke ta jefa 5 bayan dan wasanta daya ya zubar da kwallonsa.

Yanzu haka Liverpool din ta samu damar zuwa wasan karshe kuma za ta fafata da Manchester City ko kuma Everton ranar 28 ga watan Fabrairu a wasan na karshe.

Wannan ne ya hankalin Jurgen Klopp din ya karkata a kan kofin farko da yake sa ran za su dauka.