Ramires ya koma Jiangsu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ramires Santos

Dan wasan tsakiya na Chelsea, Ramires Santos ya koma kungiyar Jiangsu Suning da ke China a kan kudi fan miliyan 25.

Dan wasan, mai shekara 28, ya zo Chelsea ne daga Benfica a kan kudi fan miliyan 17 a 2010.

Ramires dai ya rattaba hannu a kan wani sabon kwantaragin da Chelsea, a watan Octoban 2015, sai dai kuma ya buga wasanni bakwai ne kacal a kakar wasan Premier.

Dan wasan wanda dan asalin Brazil ne ya taimakawa Chelsea ta ci Premier da FA Cup da gasar Champions da kuma ta Europa.

Shi dai kulob din na Jiangsu ya zo na tara a gasar manyan kungiyoyin wasan China a 2015 sannan kuma ya dauki kofin kasar na shekarar.