Novak Djokovic ya doke Roger Federer

Hakkin mallakar hoto Getty

Novak Djokovic ya doke Roger Federer gasar Australian Open ta 2016

Novak Djokovic ya kai matakin buga wasan karshe a karo na shida a gasar Australian Open bayan ya yi nasara akan Roger Federer da 6-1 6-2 3-6 6-3

Zakaran wasan Tennis din na duniya Djokovic zai fuskanci Andy Murray ko kuma Milos Raonic na Canada a wasan karshe

Dan wasan na Sabiya ya doke zakaran wasan Tennis din Biritaniya Andy Murray sau uku a wasan karshe da suka hada da wanda aka yi a bara