Kyaftin din Kamaru Stephane ya koma China

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Staphane na wasa ne da kulob din Turkiyya wato Trabzonspor

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Kamaru, Stephane Mbia, ya rattaba hannu kan kwantiragin komawa kulob din Hebei a China.

Stephane mai shekaru 29 kuma tsohon dan wasan tsakiya na kulob din Marseille, ya bi sahun dan wasan Ivory Coast Gervinho wanda ya riga ya koma taka leda a China.

Kulob din na Hebei ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, "Mun zaku mu ga yadda jarumin mai tsaron gida Mbia zai nuna iya kwarewarsa."

Shi ma dan wasan ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, "Ina alfahari da komawa kulob din Hebei China Fortune, kuma a shirye nake don murza leda a can, sai kun zo."

A ranar Laraba ne Stephane ya rattaba hannun komawa Hebei daga AS Roma.