De Bruyne zai yi jinyar makonni goma

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption De Bruyne ya koma City a kan fan miliyan 55

Dan kwallon Manchester City Kevin de Bruyne ya ce zai yi jinyar akalla makonni 10 saboda raunin da ya ji a gwiwarsa ta dama a lokacin wasansu da Everton a ranar Laraba.

Dan wasan na kasar Belgium mai shekaru 24, ya haskaka a wasan da ya ji raunin.

De Bruyne wanda tsohon dan wasan Wolfsburg ne ya ce " Zan yi jinyar kusan makonni 10."

Kenan dan wasan bai zai muga wasanni gasar Premier 13 ba da kuma zagaye na biyu a gasar zakarun Turai.

De Bruyne ya zura kwallaye 12 a kakar wasa ta bana, kuma Sergio Aguero ne kawai ya fi shi cin kwallaye.