Dembele ya sabunta kwantiragi da Tottenham

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tottenham ta sayi Dembele daga Fulham a kan kudi fam miliyan 15 a shekarar 2012

Dan wasan tsakiya na kulob din Tottenham Hotspur Mousa Dembele, ya tsawaita kwantiraginsa da kulob din na tsawon shekaru uku masu zuwa.

Mousa mai shekaru 28 dan kasar Belgium ya zura wa Tottenham kwallaye uku a wasanni 18 da ya buga wa kulob din, domin taimaka wa Spurs daukar kambun gasar Premier.

Ya shaida wa shafin intanet na kulob din cewa "Yadda muke wasa kuma kulob din ke samun ci gaba sai dai san barka."

Inda ya kara da cewa "Kowa na son ya kasance cikin 'yan wasan kulob din nan, shi yasa nake alfaharin tsawaita kwantiragi na."