Tennis: Murray da Bruno sun dauki kofi

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Jamie Murray

Jamie Murray da Bruno Soares sun dauki kofi bayan sun doke abokan karawarsu, Daniel Nestor da Radek Stepanek da ci 2 da 6 da 6 da 4 da 7 da 5.

Yanzu haka, Jamie Murray ne mutum na farko dan Birtaniya da ya taba cin kofin wasan Tennis na mutum biyu, a gasar Australian Open, a tsawon shekaru 82.

Shi kuma Soares, mai shekara 33 dan kasar Brazil ne.