Wilshere zai koma taka leda - Wenger

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jack Wilshere

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya ce dan wasansa tsakiya, Jack Wishere zai koma bakin daga a tsakiyar watan Maris.

Wenger ya ce " Jack ya fara gudu."

Shi dai Wishere bai buga wasanni ba a wannan kakar sakamakon raunin da ya ji a kasar gwiwarsa, a watan Agusta.

Wilshere ya dade yana fama da matsalar rauni a gwiwa tun da ya samu matsala a gwiwar tasa a wasannin gab da fara gasar Premier a 2011, kuma hakan ya sanya ya kwashe watanni 15 ba tare da ya taka leda ba.