Chelsea vs MK Dons: Oscar ya ci uku

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Oscar Santos

Dan wasan Chelsea, Oscar Santos ya jefa kwallaye har uku a ragar MK Dons a wasan neman buga zagaye na biyar a gasar cin kofin FA.

Tun da farko dai dan wasan wanda dan kasar Brazil ne shi ya fara daga ragar MK Don, kafin Darren Potter ya farke wa kulob dinsa.

Amma daga baya, Oscar ya kara ta biyu da ta uku a jere.

Eden Harzard ne ya ci ta hudu daga gurbin buga fanareti, yayin da Bertrand Traore ya jefa ta biyar a ragar MK Dons din.