Tennis: Djokovic ya dauki kofin Australian Open

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption djokovic ya dauki kofi

Dan wasa mai matsayi na daya, Novak Djokovic ya dauki kofi gasar wasan tennis ta Australian Open karo na shida bayan da ya kasa Andy Murray a zangon wasannin da suka buga.

Shi dai Djokovic, mai shekara 28 wanda kuma dan kasar Serbia ne ya cinye Murray da ci 6 da 1 da 7 da 5 da kuma 7 da 6.

Wannan dai shi ne karo na biyar da Andy Murray yake rashin sa'a a wasan karshe na Australian Open din, kuma hudu daga ciki, Djokovic ne yake kashe shi.