CHAN 2016: Mali ta doke Tunisia

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mai tsaron gidan Mali, Djigui Diarra

Mali ta samu nasara a kan Tunisia da ci 2 da 1, a wasan dab-da-na-kusa-da-na-karshe na gasar wasan cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan gida da ake yi a Rwanda.

Mohamed Ali ne ya fara ci wa Tunisia kwallo tun kafin aje hutun rabin lokaci.

Sai dai kuma bayan dawo wa daga hutun rabin lokaci, Aliou Dieng da Abdoulaye Diarra sun zura kwallaye biyu a ragar Tunisia, abin da ya dora Malin bisa abokiyar karawar tata.

Yanzu dai Mali ta kora Tunisia gida, kuma za ta kara da Ivory Coast ne a wasan karshe, ranar Alhamis.