John Terry zai bar Chelsea

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Terry ya buga wasanni 696 a Chelsea.

Chelsea bai sabunta kwantaragin kyaftin dinsa John Terry ba, kuma da alama dan wasan zai bar kulob din a karshen kakar wasa ta bana.

Dan wasan mai shekara 35, wanda ya koma kulob din yana dan shekara 14, ya taimakawa Chelsea wajen lashe kofuna hudu na gasar Premier, da kofunan FA guda biyar da kofin Zakarun Turai.

Terry ya ce, "A gaskiya ina son ci gaba da murza leda a Chelsea, amma na ga kulob din yana sauya alkibla."

Sai dai mai magana da yawun kulob din ya ce mai yiwuwa za a sabunta kwantaragin Terry.

Terry ya buga wasanni 696 a Chelsea.