Man City: Guardiola zai gaji Pellegrini

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pep Guardiola da Pellegrini

Pep Guardiola ya amince da kwantaragin shekaru uku na zama manajan kunigyar Manchester City, da zai fara a bazara.

Guardiola mai shekara 45 wanda shi ne kociyan Bayern Munich zai maye gurbin Manuel Pellegrini wanda zai bar kulob din ranar 30 ga watan Yuni.

Wata sanarwa da Manchester City ta fitar ta ce Pellegrini mai shekara 62 'ya goyi bayan sanarwar' da aka fitar kan barin kulob din.

Sanarwar ta ce tattaunawa da Guardiola cigaba ce kan wadda aka fara a 2012.

Shi dai Pellegrini ya zo Man City ne a 2013, kuma ya ciwo wa kulob din wasanni Premier 64 daga cikin wasanni 99 da suka buga.

Yanzu haka, Manchester City ce ta biyu a teburin gasar Premier.