Premier: An kashe Fam biliyan daya

Image caption An kashe Fam biliyan daya a Premier

Kungiyoyin gasar Premier sun kashe kudi har sama da Fam biliyan daya a musayar 'yan wasa a karo na farko a kakar wasanni.

A kakar wasa ta 2014 zuwa 2015 an kashe Fam miliyan 965, abin da ke nuna cewa na kudaden da aka kashe na wannan kakar sun fi na baya yawa.

Kungiyoyi 20 dai sun kashe Fam miliyan 130 a musayar 'yan wasan da ake kammalawa a daren ranar Litinin, a inda Newcastle ta kashe Fan miliyan 29.

Newcastle din ta rattaba hannu wajen neman Jonjo Shelvey da Andros Townsend da kuma Henr Saivet sannan kuma sun yi tayin sayen dan wasan West Brom, Saido Berahino, a kan Fam miliyan 21.