Everton ta sayi Oumar Niasse

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Martinez ya ce Oumar Niasse zai taka rawa a kungiyar.

Kungiyar Everton ta sayi dan kasar Senegal Oumar Niasse wanda ke murza leda a kungiyar Lokomotiv Moscow a kan Fam miliyan 13.5.

Dan wasan, mai shekara 25, ya zura kwallaye 13 a wasanni 23 da ya buga wa Lokomotiv a kakar wasa ta bana, kuma ya sanya hannu a kan kwantaragin shekara hudu da rabi a kungiyar Goodison Park.

Kociyan Everton Roberto Martinez ya ce, "muna farin cikin sayen Oumar kasancewarsa dan wasan da muka dade muna son saya."

Martinez ya kara da cewa Oumar zai rika dagewa wajen zura kwallaye a kulob din da dama yake da zaratan 'yan wasa.

Kulob din ya so sayen dan wasan Dynamo Kiev Andriy Yarmolenko sai dai bai yi nasara ba.

Everton ta sayi Niasse bayan dan wasansu na gaba Steven Naismith ya koma Norwich, sannan Sheffield ta karbi aron dan wasan baya Aiden McGeady ranar Laraba.