Komawa Atletico ta yi wa Falcao wuya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Radamel Falcao

Dan wasan Chelsea, Radamel Falcao bai samu damar koma wa Atletico Madrid ba a ranar Litinin lokacin da ake rufe kasuwar musayar 'yan wasa.

An ce an dai ga Falcao a birnin Madrid na Spaniya ranar Litinin yana neman koma wa La liga.

Shi dai Falcao ya buga wasa daya ne kawai a wasanni Premier, a inda ya zura kwallo daya tilo.Tun dai watan Nuwamba da ya ji rauni a cinyarsa bai sake buga wasa ba.

A lokacin yana Atletico Madrid, Falcao mai shekara 29 ya taimaka wa kulob din cin gasar Europa a 2012 da Copa del Rey a 2013. Ya kuma zura wa kulob din kwallaye 52 a wasanni 68.