Leicester: Vardy zai tsawaita kwantaragi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Leicester, Jamie Vardy

Dan wasan Leicester, Jamie Vardy yana gab da amince wa da wani sabon kwantaragin cigaba da zama a kulob din har na shekara uku da rabi.

Jamie Vardy, mai shekara 28 yana da sauran shekara biyu ya kammala kwantaragin da yake yi da kulob din amma idan aka kara masa shekara uku da rabin to zai kai har 2019 ke nan.

Vardy dai ya je Leicester ne daga Fleetwood a kan £1m a 2012 kuma ya zura wa kulob din kwallaye 20 a wasanni 34.

Jamie shi ne dan wasan da ya ci kwallaye 11 a jere a wasannin Premier na November.

Shi ne dai dan wasan da ya dara Ruud van Nistelrooy a kulob din.