Tennis: Johanna ba za ta wakilci Birtaniya ba

Image caption Johanna Konta ba za ta buga Fed Cup Tie ba

'Yar wasan Tennis 'yar kasar Birtaniya wanda ta kai wasan dab-da-na-karshe a gasar Australian Open, Johanna Konta ba za ta wakilci kasar tata ba a gasar kwallon Tennis ta mata ta duniya saboda rashin lafiya.

A farkon makon nan ne dai Johanna ta sanar da fice wa daga kungiyar wasan tennis din ta Birtaniya sakamakon rashin lafiya.

An dai zabi matashiyar nan 'yar Birtaniya, Katie Swan, mai shekara 16 a matsayin daya daga cikin wadanda za su buga wa Birtaniyar wasan tennis na mutum daya-daya.

A wannan makon ne dai za a fara gasar tennis din ta mata ta duniya a Isra'ila.