Neymar Zai gurfana a kotu kan haraji

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zargin Barcelona da zille wa biyan harajin da ya kamata a cinikin Neymar.

Dan wasan Brazil Neymar zai gurfana a gaban wata kotun Spain domin bayar da shaida a kan zargin zille wa biyan haraji da ake yi a lokacin komawarsa Barcelona a shekarar 2013.

Shugaban kungiyar ta Barcelona n yanzu da tsohon shugabanta dukkansu sun musanta aikata ba daidai ba a kan batun lokacin da suka gurfana a gaban wata kotun Madrid ranar Litinin.

Kungiyar ta Barcelona ta ce ta biya kulob din Santos na Brazil £43m wajen sayen Neymar, mai shekara 23, kuma iyayensa sun karbi Yuro miliyan 45 a cikin kudin.

Sai dai masu bincike sun yi zargin cewa kudin da aka biya wajen sayen dan wasan sun kusa kai wa Yuro miliyan 83, don haka ya kamata kungiyar ta Barcelona ta biya harajin Yuro miliyan goma sha uku.

Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu da wanda ya gada, Sandro Rosell, sun musanta cewa sun cuci ofishin karbar harajin.