Guangzhou Evergrande ta sayi Martinez £31m

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jackson Martinez ya zura kwallaye uku ne kawai cikin wasanni 22 da ya bug a Atletico.

Kungiyar kwallon kafar Guangzhou Evergrande ta kasar China ta sayi dan wasan Atletico Madrid Jackson Martinez a kan £31m.

Dan wasan, dan kasar Colombia mai shekara 29, ya sanya hannu ne a kwantaragin shekara hudu da kungiyar, kuma zai je Dubai ranar tara ga watan Fabrairu domin yin atisaye don gwajin lafiyarsa.

Martinez ya zura kwallaye uku ne kawai a wasanni 22 da ya buga wa Atletico, wadda ta saye shi daga hannun Porto a kan £24.8m a bara.

Martinez shi ne babban dan wasa na baya bayan nan da ya koma China domin murza leda.

Tsohon dan wasan Chelsea Ramires da tsofaffin masu murza leda a gasar Serie A, wato Gervinho da Fredy Guarin na cikin manyan 'yan wasan da suka koma China domin wasa a shekarar 2016.

Luiz Felipe Scolari - tsohon dan wasan Chelsea da Brazil - shi ne kociyan Guangzho.

Yanzu dai Martinez zai hadu da tsofaffin 'yan wasan Tottenham Paulinho da Robinho a sabuwar kungiyar tasa.