Muna kaunar Pellegrini, in ji 'yan wasan Man City

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Joe Hart ya ce sun je City ne domin daukar kofuna.

Golan Manchester City players Joe Hart ya ce suna "kaunar" Manuel Pellegrini a matsayin kociyan kungiyar.

Za a maye gurbin Pellegrini, dan kasar Chile, da Pep Guardiola a karshen kakar wasa ta bana, bayan da kungiyar ta shiga yanayi na rashin tabbas dangane da lashe kofuna hudu a bana.

A ranar Litinin ne aka sanar da cewa Guardiola zai maye gurbin Pellegrini, kwana guda kafin City ta doke Sunderland da ci 1-0 a gasar Premier ta Ingila.

Amma Hart ya ce, "Muna son Pellegrini a matsayin kociyanmu, muna kuma goyon bayansa. Mun zo wannan kungiya ne domin mu rika daukar kofuna. Shi ma Manuel ya zo nan ne domin ya lashe kofuna."

Hart, mai shekara 28, ya hana a zura musu kwallo sau da dama a wasan da suka yi a Stadium of Light, inda kwallon da Sergio Aguero ya zura tun daga fara wasan, ta sa suka yi nasara a kan Sunderland.